ABNA24 : Majiyar ta kara da cewa; Makaman na Syria sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami da jiragen sama na yaki na HKI suka harba, tare da kakabo da dama daga cikinsu.
Tashar talabijin din ‘al-Manar” ta kasar Lebanon ta ambaci cewa; Daya daga cikin makamai masu linzamin na kasar Syria ya bi sawun jirgin saman ‘yan sahayoniya na yaki har cikin sararin samaniyar kasar Lebanon.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da jiragen yakin HKI su ke kai hari akan Syria, inda sojojin kasar kan mayar da martani da kuma kakkabo makamai masu linzami da dama.
342/